Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Labarin ya kara da cewa mako guda kenan da shigowar sojojin kasar ta Denmark su 90 kasar ta Mali, gwamnatin sojojin ta bada wannan sanarwan.
Sai dai gwamnatocin kasashen turai wadanda suke da sojojin kasar Ta Mali, musamman kasar Faransa sunce sun fara tattauna batun shigar sojojin kasar Denmark kasar ta Mali tun gwamnatin da ta shude.
MDD tana da rundunar sojojinta na tabbatar da zaman lafiya a kasar ta Mali mai suna (MINUSMA). Kafin haka tun shekara ta 2013 ne kasar Faransa ta jibge dubban sojojinta a arewacin kasar Mali da sunan yaki da ayyukan ta’addanci.
342/